Tashe tashen hankula Kongo gabanin zaben gama gari a ranar lahadi | Labarai | DW | 25.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula Kongo gabanin zaben gama gari a ranar lahadi

Kwanaki biyar gabanin zabukan shugaban kasa da na ´yan majalisar dokoki da za´a gudanar a kasar JDK, an yi mummunar arangama tsakanin dubban magoya bayan ´yan adawa da ´yan sanda a birnin Kinshasa. ´Yan adawan sun ta jifar ´yan sanda da duwatsu da bama-baman kwalaba kana kuma sun yi kira da a dage ranar kada kuri´ar. Su kuma a nasu bangare ´yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kulake akan gungun masu zanga-zangar. Don ba da kariya a lokacin zaben rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr ta tura sojoji kusan 800 zuwa Kinshasa.