Tashe tashen hankula akan iyakar Chadi da Sudan | Labarai | DW | 18.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula akan iyakar Chadi da Sudan

Kasar Chadi ta zargi makwabciyarta Sudan da hannu a wani harin da aka kai kan iyakarta da ya halaka sama da mutane 100 sannan wasu 30 suka jikata a garin Adre. Gwamnatin Chadi ta ce ta na da ´yancin fatattakar maharan har cikin kasar Sudan. Kakakin gwamnati a birnin Ndjamena ya ce wasu sojojin ´yan tawaye da suka hada kai da wata sabuwar kungiya da ake kira Rally For Democracy and Liberty RDL suka kai harin. Chadi dai na zargin cewa gwamnatin Sudan na amfani da ´ya´yan kungiyar ta RDL a matsayin sojojin sa kai.