Tashe tashen hankula a yankin kan iyakar Turkiya da Iraƙi | Labarai | DW | 08.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a yankin kan iyakar Turkiya da Iraƙi

Sojin Turkiya daya ya rasu sannan wasu 3 sun samu raunuka a fashewar wata nakiyar karkashin kasa a lardin Diyarbakir dake kudu maso gabashin kasar. Hakan ya zo ne kwana guda daya bayan da ´yan tawayen Kurdawa na kungiyar awaren PKK suka halaka sojojin Turkiya 13 a wani abin da ke zama asara mafi yawa da rundunar Turkiya ta taba yi a fafatawar da take yi da ´yan tawayen. FM Rejep Tayyip Erdogan yayi tir da harin yana mai cewa yakin da Turkiya ke yi da ´yan ta´adda zai dauki wani sabon salo. Tsohon hafsan sojin Turkiya Janar Haldun Solmaztürk ya bayyana halin da ake ciki da cewa mai damuwa ne.

Solmaztürk:

“Wannan ci-gaba ne mai ban tsoro. Ina fata gwamnatin Turkiya da babban kwamandan dakarun kasar zasu dauki halin da ake da muhimmanci. Domin hakan ya dade yana faruwa.”