Tashe tashen hankula a ranar bukin Ashura | Labarai | DW | 10.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a ranar bukin Ashura

Akalla mutane 35 suka rigamu gidan gaskiya sannan wasu da dama suka jikata a tashe tashen hankula da suka wakana lokacin bukukuwan Ashura a Pakistan a jiya alhamis. Ranar Asura dai tana da tsarki ga mabiya darikar shi´a. Daukacin wadanda suka mutum dai sun rasa rayukansu ne a wani harin kunar bakin wake da aka kai kan wani gangamin ´yan shi´a dake garin Hangu a can arewa maso yammacin Pakistan. A Afghanistan kuma wato makwabciyar Pakistan, akalla mutane 5 suka rasu sannan fiye da 20 suka samu raunuka a wata arangama da aka yi tsakanin ´yan shi´at da ´yan sunni a bukin Ashurar a garin Herat dake yammacin kasar. Bukin Ashura dai na tunawa ne da rasuwar jikan Annabi Mohammed SAW, wato Immam Hussein a cikin karni na 7.