1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Mogadishu

April 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuON

Wata hukumar kare hakkin bil adama a kasar Somalia tace kwanaki hudu na kazamin fada a birnin Mogadishu sunyi sanadiyar rayukansu mutane akalla 381 wasu kuma 565 suka jikkata.

Shugaban hukumar kare hakkin bil adama ta Elman Sudan Ali Ahmed yace har yanzu akwai gwarwakin jamaa da dama kann titunan birnin Mogadishu.

Hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD tace akalla mutane 47,000 suka tsere da mogadishu cikin kwanaki 10 da suka shige.

Tun kuma watan fabrairu mutane 100,000 suka fice daga Mogadishu yawancinsu mata da yara kanana.