1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a kudancin Afghanistan

August 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bunw
Wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota ya halaka akalla fararen hula 21 ciki har da kananan yara a wata kasuwa dake lardin Kandahar na kudancin Afghanistan. Wasu mutane 13 kuma sun samu munanan raunuka. Kamar yadda ma´aikatar cikin gida ta nunar maharin ya auna fararen hula ne domin ba wuraren binciken ababan hawa na gwamnati ko na kungiyar tsaro ta NATO a kasuwar. Harin wanda ke daya daga cikin munanan hare hare da aka kai a yankin a cikin watanni baya-bayan nan ya zo ne cikin mako guda bayan da NATO ta karbi ragamar tsaron kudancin Afghanistan daga rundunar kawance karkashin jagorancin Amirka. A wani labarin kuma wasu da ake zargi mayakan Taliban ne sun kashe sojojin NATO guda 3 sannan suka raunata 6 a wani harin gurnati da suka kai a kudancin Afghanistan din.