Tashe tashen hankula a Kongo gabanin zabe a ranar lahadi | Labarai | DW | 27.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Kongo gabanin zabe a ranar lahadi

Kwanaki 3 gabanin zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za´a gudanar a kasar JDK, an kashe mutane 4 a wata musayar wuta da aka yi tsakanin magoya bayan ´yan takaran shugaban kasa biyu wato Josef Kabila da Jean Pierre Bemba. Dukkan sassan biyu da ba sa ga maciji na zargin juna da laifin barkewar fadan a garin Gbadolite dake arewacin kasar a jiya alhamis. Daga cikin wadanda aka kashe a hargitsin kamar yadda wata tashar radiyo ta nunar akwai wani sojin sa kai mai goyon bayan dan adawa Jean-Pierre Bemba.