1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TASHE TASHEN HANKULA A KASAR GEORGI

May 6, 2004

WAN NAN HOTON SHUGABA ASLAN NE YAYIN DA YAKE JAWABI GA YAN JARIDA A RANAR LARABA DATA GABATA:

https://p.dw.com/p/Bvjv
Hoto: AP

Awowi kadan bayan gudanar da zanga zangar lumana ta neman shugaban yankin Adzharian na kasar Georgia Aslan Abashidze yin hijira izuwa kasar Russia, a yau alhamis faraministan kasar Zurab Zhvania ya bayar da sanarwar cewa nan da makonni shida za a gudanar da zabe a wan nan gunduma tare da bude taron sulhu na cimma dai dai to a tsakanin yankunan guda biyu.

Jim kadan bayan tashin Abashidze izuwa russia Shugaban kasar na Georgia Mikail Saakashvilli ya kai wata ziyara ta musanman izuwa yankin na Adzharia.

A lokacin wan nan ziyarar ne shugaba Mikail ya bayar da sanarwar cewa yin hijirar Aslan izuwa kasar Russia tare da wani jamian tsaron kasar Igor Ivanov wata kafa ce data bude sabon babi na tattauna sulhu dangane da samar da zaman lafiya a fadin kasar baki daya.

Wadan nan yan zanga zanga a baya dai an shirye cewa zasuyi bore ne ga gwamnatin kasar ta Georgia amma kuma daga baya sai ta rikide izuwa zanga zanga da ake yabon shugaba mikail a hannu daya kuma da murnar ficewar Aslan Abashidze izuwa kasar ta Russia.

Sakamakon wan nan sabon ci gaba da aka samu rahotanni sun shaidar da cewa shugaba Mikail a yanzu haka yaci alwashin daukar matakan hade yankunan nan guda biyu da suka dare sakamakon yaki a shekara ta 1990. Wadan nan yankuna dai sun hadar da yankin Abkhazia da kuma Kudancin Assetia.

Yin murabus na Aslan Abashidze daga shugabancin yankin na Adzharian tare da ficewa daga kasar izuwa kasar Russia a mat´sayin dan gudun hijira abune da gwamnatin ta Mikail ta bayyana shi a matsayin nasara musanmamma bisa laakari da irin makuden kudaden dake shigo aljihun gwamnati daga tashar ruwa dake yankin.

A yanzu haka dai rahotanni sun shaidar da cewa jamian tsaron kasar ta Georgia tuni suka rarrabu a yankin na Adzharian don tabbatar da harkokin tsaro a ofisoshi da bankuna da kuma maikatun gwamnati dake yankin.

A can baya dai kafin Abashidze ya bar yankin na Adzharian sai daya bawa magoya bayan sa umarnin karya wata babbar gada data hade yankin da ragowar yankunan kasar ta Georgia bisa manufar kare afkowar dakarun sojin kasar izuwa yankin a cikin sauki.

Har ila yau shugaba Aslan ya kuma bayar da umarni na a karya hanyoyin jiragen kasa dake shigowa cikin yankin.

Daukar wan nan mataki a yanzu haka ya jefa dubbannin mutanen yankin cikin rudani da tararrabi na fuskantar wahalhalu dangane da shigo da kayan abinci da kuma abubuwan bukatun yau da kullum izuwa yankin.

Rahotanni dai sun nunar da cewa kafin barin Abashidze gida a safiyar yau alhamis,wanda hakan ya kawo karshen rikici da yake haifarwa a yankin na tsawon shekaru 13 sai da wani dan majalisar dokokin kasar ya dauko kujerar sa daga cikin gidan sa aka kone ta kurmus,wanda yin hakan a ganin sa shine ya kawo karshen mulkin sa a yankin na Adzharian.

IBRAHIM SANI.