Tashe tashen hankula a Ivory Coast | Labarai | DW | 17.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Ivory Coast

Jamiyar dake mulki a kasar ivory Coast,tace zata janye daga shirin zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta kirkiro da shi ga kasar ,wanda hakan ya kara janyo rudani game da kokarin kasashen duniya na kawo karshen rikicin kasar.Jamiyar shugaba Laurent Gbagbo ta FPI ta bada wannan sanarwa yayinda magoya bayan shugaban kasar suka gudanar da zanga zanga game da kira da masu shiga tsakani sukayi na rusa majalisar dokokin kasar.Sun kuma yi kira da janyewar dakarun MDD 7,000 dake aiyukan wanzar da zaman lafiya a kasar mai arzikin koko wacce ta rabe gida 2 tun yakin basasa na 2002 tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati.