TASHE TASHEN HANKULA A IRAQI. | Siyasa | DW | 09.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TASHE TASHEN HANKULA A IRAQI.

Kwanaki biyar kenan ana ta dauki ba dadi a birnin najaf dake kasar iraqi,tsakanin yan darikar shiawa da kuma dakarun sojin amurka dake kasar.

Wannan rikici da yaki ci yaki cinyewa a yau dai rahotanni sun tabbatar da cewa yan shiawa sama da dari uku da sittin ne suka rasa rayukansu,sai kuma wasu sojin amurka guda hudu da suka rasa nasu rayukan.

Muqtadr Sadr shugaban shiawan na iraqi,a wani taro da suka gudanar a wani masallaci dake najaf,ya bayyanawa jamaarsa cewa zasu cigaba da yakar sojin amurka har sai inda karfin su ya kare,haka kuma ba zai bar najaf ba duk da cewa shi suke neman capkewa.

Yanzu dai garin na najaf banda karar tashin boma bomai da harbe harbe bindigogi,tare kuma da karar jiragen yaki,babu abinda ake ji,sai kuma kone konen wurare da ake tayi.

A jiya lahadi ne,prime ministan kasar iraqi mai rikon kwarya Iyad Allawi,ya kai ziyarar ba zato izuwa garin na najaf,don ganewa idon sa barnar dake wanzuwa a garin.

Mr Allawi ya bayyana rashin jin dadin sa matuka akan wannan rikici,inda a take ya bukaci shiaawan dasu ajiye makaman su,su daina yaki da sojin amurka wanda yace ba don yaki suka zo ba sai don wanzar da zaman lafiya.

Shi kuwa shugaban shiawan Muqtadr Sadr ya jaddadawa magoya bayan sa da kada su kuskura su ajiye makaman nasu har sai sun ga bayan sojin amurkan.

A wata sabuwa kuma a can arewacin bagadaza a wani kauye mai suna balad ruz,an fuskanci tashin bomb daya halaka yan sandan kasar bakwai,tare kuma da raunana wasu mutane goma sha bakwai.

A yau dai rahotanni sun tabbatar da cewa mutane ashirin da hudu ne suka rasa rayukansu a birane daban daban na kasar banda najaf,sakamakon tashe tashen hankula da ake ta fuskanta a fadin kasar.

Kamar dai yadda hankalin mutane mazauna birnin bagadaza yake a tashe a yanzu haka,sakamakon harba gurneti da yan sari ka noke suka yi tayi cikin dare,wanda har yayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu.

Baya ga wannan tashe tashen hankula a kasar sai kuma gashi babbar kotun kasar iraqin karkashin shugabancin Zuhair Al Maliki ta fidda takardar sammacin da zaa kamo Ahmed Challabi wani jamii da kasar amurka ke ji dashi a da da kuma dan uwansa Salem Challabi alkalin dake shugabantar kotu ta musamman mai gudanar da shariar tsohon shugaban iraqi Saddam Husseini domin gurfanar dasu a gaban sharia.

Kamar yadda takardar ta bayyana ana tuhumar Ahmed Challabi ne da laifin buga jabun kudade shi kuwa Salem Challabi ana tuhumar sa ne da laifin kisan kai.

Sai dai kuma wadannan jamiai da a yanzu basa kasar iraqin sun karyata wannan zargi da ake musu da cewa ba wani abu bane illa siyasa kawai,shi dai Salem Challabi,ya ce Zuhair Al Maliki daya bada wannan sammaci dama ya dade dayin suka ga tsarin da ake bi na tuhumar Saddam Husseini tsarin da shi yake jagoranta.

Haka kuma ya cigaba da cewa wannan tuhuma da ake masa ba wani abu bane illa zargin karya domin kuwa kamar yadda yace yayi barazana ne kawai ga rayuwar wani wanda daga baya aka kashe bada sanin sa ba.

Shi kuwa Ahmed Challabi cewa yayi wannan shiri ne na makiyansu dake so suga bayansu,musamman ma ga zargin da ake masa na zama dan leken asirin kasar iran.

Wadannan jamiai dai sun ce zasu dawo izuwa iraqi domin su fuskanci wannan tuhuma da ake musu don warware zargin da ake musu.

Maryam L.Dalhatu.