1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankula a Iraqi a ranar bukin Ashura

January 19, 2008
https://p.dw.com/p/Cuo3

Aƙalla mutane biyu sun rasu sannan wasu biyar sun jikata lokacin da wasu bama-bamai biyu da aka ɓoye ƙarƙashin shara suka tashi a wurin da ´yan shi´a ke gudanar da bukin Ashoura a arewacin Iraqi. Bama-baman sun fashe ne a birnin Kirkuk mai arzikin man fetir da ke arewacin Iraqi lokacin da mabiya ɗarikar shi´a ke gudanar da wannan buki da ke da muhimmanci ga musulmi. Yanzu haka dai hukumomin ƙasar sun tsaurara matakan tsaro yayin da mutane kimanin miliyan biyu suka hallara a birnin Karbala don gudanar da wannan buki. Ana cikin halin ɗar-ɗar bayan da mutane kimanin 68 suka rasu a jiya juma´a a wani taho-mu-gama da aka yi tsakanin ´yan sanda da wasu mutane da ake zargin cewa ´ya´yan wata ƙungiyar asiri ce ta ´yan shi´a biranen Nasiriya da Basra.