Tashe tashen hankula a Iraki | Labarai | DW | 01.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Iraki

Akalla mutane 20 sun rigamu gidan gaskiya a wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota a Basra birni na biyu mafi girma a Iraqi. Hukumomi sun ce wasu mutane 45 sun samu rauni a harin bam din. An kai harin ne a wata unguwa mai cike da kantuna a daidai lokacin da mutane ke sayayya a ranakun karshe na azumin watan ramadana. A wani labarin kuma sojojin Amirka 6 sun mutu a fashewar wasu bama-bamai biyu da aka dana a gefen hanya a kusa da birnin Bagadaza. Yayin da sojan Amirka daya ya gamu da ajalinsa a fashewar wani bam a kusa da birnin Falluja.