Tashe tashen hankula a Iraki | Labarai | DW | 03.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Iraki

Sojojin Amirka 14 suka rasu sakamakon wasu hare hare guda uku a kasar Iraqi. Mafi muni daga cikin hare haren shi ne wani harin bam da aka dana a gefen hanya a kusa da birnin Fallujah wanda ya halaka sojojin Amirka 10 sannan 11 suka samu raunuka. Birnin Fallujah dai ya kasance wani dandanlin wani mummunan gumurzu tun bayan kifar da gwamnatin Saddam Hussein shekaru 2 da rabi da suka wuce, to amma a ´yan watannin nan zaman lafiya ya dawo a birnin. Sauran sojoji 4 kuma sun mutu ne a wasu hare hare dabam-dabam a jiya juma´a. A kuma halin da ake ciki da yawa daga cikin shugabannin siyasar Amirka na kira ga shugaba Bush da ya janye dakarun kasar daga Iraqi. A kuma can yamma da birnin Bagadaza sojojin Amira da na Iraqi sun kaddamar da wani farmaki akan ´yan tawaye