1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Iraki

April 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0P

An kai wani harin bam akan ayarin motocin sojojin kasashen duniya a Iraqi, inda aka halaka mutum 4. Ma´aikatar tsaron Italiya ta ce sojoji 3 ´yan kasar ne yayin da daya dan kasar Romaniya. Wani soja daya daga Italiya na cikin wani mawuyacin hali sakamakon harin da aka kai kan wani ayarin motoci 4 a garin Nasiriyya, inda Italiya ta girke sojojinta sama da dubu 2. Shugaban Italiya Carlo Azeglio Ciampi ya ba da wata sanarwa wadda a ciki ya nuna kaduwarsa game da wannan hari. A kuma can garin Baquba ´yan tawaye sun halaka ´yan sandan Iraqi 4. A wani labarin kuma wasu ´yan bindiga a birnin Bagadaza sun harbe ´yar´uwar sabon mataimakin shugaban Iraqi dan Sunni, har lahira. An halaka Mayson al-Hashimi yau alhamis a lokacin da ta ke barin gidanta. A ranar asabar da ta wuce majalisar dokokin Iraqi ta nada dan´uwanta Tariq al-Hashimi a mukamin mataimakin shugaban kasa. Kimanin makonni biyu da suka wuce aka harbe dan´uwanta har lahira.