Tashe tashen hankula a Iraki sun halaka akalla mutane 120 | Labarai | DW | 06.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Iraki sun halaka akalla mutane 120

Makonni 3 bayan zaben ´yan majalisar dokokin Iraqi, tashe tashen hankula sun tabarbare a cikin kasar. Akalla mutane 120 aka kashe sannan kimanin 180 suka samu raunuka a jerin hare-hare da aka kai jiya alhamis a fadin kasar. A birnin Ramadi inda ´yan Sunni suka fi rinjaye wani dan kunar bakin wake ya halaka mutane 67 lokacin da ya ta da bam a wani ofishin daukar ´yan sanda aiki. Yayin da a birnin Karbala mai tsarki ga mabiya Shi´a, akalla mutane 44 suka kwanta dama sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai kusa da masallacin Imam Hussein. A biranen Baquba da Bagadaza ma an kai wasu hare haren. A kuma halin da ake ciki shugaba Jalal Talabani ya tabbatar da cewa tashe tashen hankulan ba zasu hana kafa gwamnatin hadin kan kasa ba. Hukumar zaben kasar ta ce kafin ranar 9 ga watannan na janeru, zata ba da sakamakon karshe na zaben ´yan majalisar dokokin.