Tashe tashen hankula a Iraki na karuwa a kullum | Labarai | DW | 31.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Iraki na karuwa a kullum

Har yanzu ba wanda ya san ranar da za´a kawo karshen tashe tashen hankula a kasar Iraqi. Jerin hare hare da aka fuskanta a jiya litinin afadin kasar sun yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 60. An kai hari mafi muni ne a unguwar ´yan shi´a wato Sadr City dake birnin Bagadaza, inda wani harin bam da aka kai ya halaka akalla mutane 32 da suka je neman aiki don samun abin sakawa bakin salati. A cikin wannan wata na oktoba rundunar sojin Amirka ta yi rashin sojoji sama da 100, wanda hakan shine asara mafi yawa cikin shekaru 2 da Amirka ta yi a Iraqi. Hakan dai ya ta da muhawwara a cikin kasar ta Amirka musamman ta masu adawa da yaki.