Tashe tashen hankula a Iraƙi sun yi sanadiyar mutuwar mutane 120 | Labarai | DW | 07.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Iraƙi sun yi sanadiyar mutuwar mutane 120

Akalla mutane 120 aka kashe a hare haren kunar bakin wake da aka kai a arewacin Iraqi a jiya da daddare da kuma yau da safe. Kamar yadda wadanda suka shaida abin da ya faru da kuma majiyoyin asibiti suka nunar, akalla ´yan Iraqi 100 ne aka kashe yau asabar sannan aka jiwa sama da 80 rauni lokacin da wani bam a cikin wata babbar mota yayi bindiga a cikin wata kasuwa da ke garin Tuz Khurmato da ke lardin Tikrit. A jiya da yamma mutane 20 suka rasu lokacin wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a cikin masu jana´iza a a Khanaqin mai tazarar kilomita 180 arewa maso gabashin Bagadaza. A kuma yau asabar rundunar sojin Amirka ta ce an kashe akalla sojojin ta 4 sannan aka jiwa 6 rauni a fadin kasar ta Iraqi.