Tashe tashen hankula a Chadi | Labarai | DW | 10.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Chadi

Wani rahoton hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD ya baiyana cewa akalla mutane 400 ne sojin sa kai na Janjaweed suka kashe a gabacin Chadi.

Rahoton yace yan janjaweed sun kai hare hare a bakin iyaka Sudan da Chadi a ranar 31 ga watan maris inda suka halaka wadannan mutane,yayinda sukayiwa kauyunksu kawanya

Tunda farko dai jamian kasar chadi sunce mutane 65 ne suka rasa rayukansu ammam kuma sunce akwai yiwuwar yawansu zai karu.

Komishian kula da yan gudun hijirar yace mafi yawa na wadanda aka kashe an rigaya an bizne su saboda haka babu dama a tabbatar yawansu.