1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a birnin Kandahar na Afghanistan

January 15, 2006
https://p.dw.com/p/BvC8

Mutane 3 ciki har da dan Kanada daya sun rasu sannan akalla 12 sun jikata a wani harin bam da aka kai kan wani ayarin motocin sojin Kanada a kudancin Afghanistan. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce wani dan harin kunar bakin wake ya ta da bam a jikinsa a lokacin da ayarin motocin suka zo wucewa a birnin Kandahar. Wani kakakin kungiyar Taliban ya ce kungiyarsa ta kai harin a birnin wanda ya taba kasancewa sansanin masu ta da kayar baya a Afghanistan. Har yanzu dai ana yawaita kai hare-haren kunar bakin wake akan sojojin Afghanista da kuma na rundunar kasa da kasa dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar.