Tashe tashen hankula a Afghanistan | Labarai | DW | 20.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Afghanistan

Rahatonnin da ba´a tabbatar da su ba sun ce dakarun Amirka sun kame babban kwamandan kungiyar Taliban Mullah Dadullah. Tun bayan hambarad da gwamnatin Taliban a karshen shekara ta 2001, Amirka ke farautar Dadullah. Su ma a nasu bangaren hukumomin Afghanistan sun ce sun kame manyan kwamandojin Taliban guda biyu. A kuma halin da ake ciki dakarun Afghanistan na ci-gaba da farautar ´yan tawaye a kudancin kasar. Kimanin mutane 100 aka kashe sakamakon mummunan fadan da aka shafe kwanaki biyu ana yi tsakanin ´yan tawayen Taliban da dakarun gwamnatin Afghanistan. A cikin watannin da suka wuce mayakan Taliban sun tsananta kai hare hare akan dakarun kasashen ketare da kuma na gwamnatin Afghanistan. A cikin watanni kalilan masu zuwa ake sa ran isar karin dubban dakarun kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan.