Tashe tashen hankula a ƙasar Afghanistan | Labarai | DW | 30.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a ƙasar Afghanistan

Jami´ai a lardin Helmand na kasar Afghanistan sun ce wani hari da jiragen saman yakin dakarun kawance karkashin jagorancin Amirka suka kai ya halaka ´yan tawayen Taliban 39, to amma harin ya janyo asarar rayukan fararen hula akalla 8. Shugaban ´yan sanda na lardin Helmand ya ce mayakan Taliban ne suka yi kokarin yiwa wani ayarin sojojin Amirka da na Afghanistan kwantan bauna. Kawo yanzu jami´an kungiyar tsaro ta NATO da na Amirka ba su ce uffan game da wannan lamari ba. A kwanakin baya shugaban Hamid Karzai ya zargi dakarun kawancen da rashin sanin makaman aiki wanda hakan ke janyo yawaitan mutuwar fararen hula a hare haren da suke kaiwa cikin kasar.