1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashar Sanduwa ta Kigali

October 26, 2005

A ranar 26 ga watan oktoban 1965 DW ta kafa tashar yada shirye-shiryenta ta Kigali

https://p.dw.com/p/Bu4b
Kigali
Kigali

Daya daga cikin dalilan da suka sanya tashar DW ta tsayar da shawarar kafa tashar sanduwar a Kigali, fadar mulkin kasar Ruwanda, saboda kwanciyar hankali da kasar ke da shi da kuma kakkarfar dangantakarta da Jamus a wancan lokaci. Kimanin shekaru biyu aka yi ana hada-hadar kafa tashar sanduwar. A lokacin da yake bayani game da haka Walter Bürger daya daga cikin magabatan da suka sa ido akan wannan manufa a shekara ta 1963 cewa yayi:

Kai-da-komon a wancan lokaci ya zama tamkar wani yawon duniya ne. Mutum zai tashi daga nan Jamus zuwa kasar Kongo, tare da ya da zango a kasashen Girka da Masar da Uganda da kuma Burundi, inda zai canza jirgi domin ci gaba da tafiya zuwa Kigali, birnin da a wancan lokaci ba ya da wani takamaiman filin saukar jiragen sama.“

A tsakanin tsaunuka masu tarin yawa da kasar Ruwanda ke da su an zabi tsaunin Kinyinya dake a tazarar kilomita 15 a arewa da fadar mulki ta Kigali. An yi amfani da wannan tashar domin yada shirye-shirye ta kann mitoci masu gajeren zango daga nan Jamus zuwa sauran sassa na duniya, musamman ma kasashen Afurka ta yadda mutum zai iya jin shirye-shiryen garau ba tare da wata hayaniya ba. To sai dai kuma DW ba kawai ta kafa tashar sanduwa ne don amfanin kanta kadai ba, su ma gidajen rediyon kasar Ruwanda sun kasance daga cikin masu cin gajiyarta, kuma DW ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa wadannan tashoshi na cikin gida. Kuma har yau akwai kakkarfar alaka tsakanin DW da gidajen rediyo da na telebijin kasar dake can kuryar tsakiyar nahiyar Afurka, inda take ci gaba da ba da horo ga ‚yan jarida da injiniyoyi daga Ruwanda. Bayan kafa wannan tasha dai ana iya kama gidan rediyon DW garau ba hayaniya a kusan dukkan sassa na nahiyar Afurka. An ci gaba da samun wannan gagarumar nasara har ya zuwa lokacin da rikicin kasar ya barke a shekarar 1994, inda a cikin kiftawa da Bisimillah aka kashe ‚yan Tutsi kimanin dubu 800. Ma’aikatan DW dake kula da tashar sanduwar sun shiga hali na kaka-nika-yi kuma sai bayan mako daya cir dakarun sojan kasar Belgium suka samu kafar ceto su. Watanni uku bayan wannan ta’asa ta kisan kiyashi sabuwar gwamnatin Ruwanda ta gabatar da roki domin sake kama aikin tashar ta yadda za a samu kafar shawo kann ‚yan gudun hijirar kasar su koma gida daga tsofuwar kasar Zaire. A cikin dan gajeren lokaci aka kammala gyare-gyaren da ake bukata domin kama aikin tashar, inda a sakamakon sabuntata da aka yi a yanzun DW ke da ikon yada shirye-shiryenta zuwa kusan dukkan sassa na duniya ba tare da ka ce na ce ba.