1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarzomar Tunisia da Masar darasi ne ga Afirka

January 30, 2011

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya shawarci shugabannin Afirka su ɗauki darasi daga boren jama'ar Tunisiya da Masar.

https://p.dw.com/p/107YC
Shugaban Faransa Nicolas SarkozyHoto: AP

A jawabin da ya yi ga taron kolin shugabannin Afirka Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya jinjinawa ra'ayin neman sauyi da al'umar Masar da kuma Tunisiya suka nuna. Shugaban na Faransa wanda tun da farko ya fuskanci matsin lamba a cikin gida bisa goyon bayan da ya nuna ga hamɓararren shugaban Tunisiya Zine el Abidine Ben Ali a lokacin tarzomar yace Faransa na martaba 'yancin kowace ƙasa a matsayinta na mai dogaro da kanta, to amma akwai wasu ɗabi'u waɗanda suka shafi mu'amalar ƙasa da ƙasa. Yana mai cewa wajibi ne shugabanni sun yi la'akari da hakan. Jawabinsa na sa ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyar gamaiyar Afirka ta zaɓi shugaban ƙasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema wanda ya yi ƙaurin suna wajen kama karya a matsayin sabon shugaban ƙungiyar ta AU. Sarkozy yace a wannan zamanin shugabanni ba za su iya cigaba da irin yadda suka yi mulki a baya ba. Yana mai cewa Ko dai ka sauya ne ko kuma sauyi yayi gaba da kai.

Afrikanische Union
Taron kolin shugabanin AfirkaHoto: picture-alliance/ dpa

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala

Edita: Usman Shehu Usman