Tarzomar matasa a Farsansa ta fara yin sauki | Labarai | DW | 11.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tarzomar matasa a Farsansa ta fara yin sauki

Ma´aikatar harkokin cikin gidan Faransa ta ce ta fara gudanar da bincike kan wasu ´yan sandan kwantar da tarzoma 8 bisa zargin dukar wani a lokacin tarzoma. Tashe-tashen hankula sun barke a biranen Faransa ne bayan mutuwar wasu matasa biyu lokacin da suke tserewa ´yan sanda makonni biyu da suka wuce. To sai dai yanzu kurar rikicin ta fara lafawa bayan da gwamnati ta farfado da wata tsohuwar dokar ta-baci wadda ta ba kananan hukumomi ikon kafa dokar hana matasa fitar dare. A lokacin da yake magana da manema labarai yayin wata ziyarar aiki da FM Spain Jose Luis Zapatero ya kaiwa birnin Paris, shugaba Jaques Chirac ya ce dole ne kasar ta koyi darasi daga tarzomar ta cikin dare kuma ta gaggauta nemo hanyoyin magance matsalolin tun daga toshi.