Tarzoma a yankin Magreb | Siyasa | DW | 05.02.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tarzoma a yankin Magreb

Ayyukan tarzoma suna karuwa a yankunan arewacin Afirka

default

Shugaban Algeria,Abdelaziz Bouteflika


A daidai lokacin da aka shiga wannan sabuwar shekara ma, babu wani canji da aka samu game da yawan hare-haren da yan takife suke kaiwa kasashe na yankin arewacin Afrika, wato kasashen yankin Maghreb. A farkon watan Janairu alal misali, yan kunar-bakin-wake sun tayar da bom da suka daurawa kansu a garin Naciria dake arewacin Algeria, inda suka kashe mutane hudu. Tun a tsakiyar watan Disamba na bara, yan tarzoman suka kai hare-hare guda biyu a Algiers, inda hukumomi suka ce akalla mutane arba'in da daya ne suka mutu, cikin su har da ma'aikatan majalisar dinkin duniya goma sha bakwai. A wannan lokaci, kungiyar yan tarzoma ta Al-Qaeda ta yankin Maghreb tace ita take da alhzakin kai wadannan hare-hare. Umaru Aliyu yana dauke da karin bayani.


Kungiyar al-Qaeda ta yankin Mahgreb, wadda ƙungiyar ce ta musulmi da ba'a daɗe da kafa ta a yankin ba, tsakanin ɗan ƙanƙanen lokaci ta samarwa kanta suna, sakamakon hare-hare na rashin imani da zubar da jini a ƙasashen Algeria da Mauretania. A halion yanzu ma, wannan ƙungiya ta zama wani ɓangare na al'amuran siyasa a arewacin Afrika. A sakamakon hare-haren watannin baya, an lura da cewar ƙungiyar ta yan tarzoma, yanzu dai ta sami gindin zama sosai a yankin na Maghreb, musmaman a Algeria. A watan Aprilu da Dismaba na bara, aiyukan tarzoma sun sake komawa birnin Algiers, bayan tsayawar da aka samu na watanni da dama. A watan Aprilu na bara, akalla mutane arba'in ne suka mutu, sakamakon harin bom da aka kaiwa majalisar dokokin Algeria. Shi kansa shugaban ƙasa, Abdulaziz Bouteflika, da kyar ya tsallake rijiya da baya a watan Satumba, lokacin da yan tarzoman suka yi ƙoƙarin ɗaukar ransa. A baya-bayan nan, hare-haren na yan tarzoman ƙasar Algeria, basu tsaya kawai kan hukumomi ko gine-ginen gwmanati ba. A watan Disamba sun kai hari kan ofisoshin hukumar yan gudun hijira ta majalisar ɗinkin duniya dake Algiers. Bugu da ƙari kuma, kungiyar ta al-Qaeda a yankin Maghreb tana maida hankali ga hare-haren nata kan gine gine na Yahudawa da na Kiristoci. A makon jiya ne alal misali, mutane biyu suka mutu, lokacin harbe-harbe a gaban ofishin jakadancin Israila a Nouakchott, babban birnin ƙasar Mauretania. Yar jaridar ƙasar Algeria, Baya Glacemi tace ba kamar a lokacin yaƙin basasan Algeria ba, a wannan karo, aiyukan tarzoman sun shafi yankin arewacin Afrika ne baki daya. Dalilin haka, shine rashin gamsuwa daga matasa, waɗanda suke taka muhimiyar rawa a tashhe-tashen hankulan na wannan karo.


Tace a farkon shekaru na casa'in, matasa da suka shigar da kansu a gwagwarmayar neman yancin Algeria, sun kasance da wani buri, kuma suna da wata aƙida. Waɗannan matasa masu kishin Islama ne da suka yi gwagwarmayar kare manufofin su. To amma a yau, shin matashi ɗan shekaru goma sha biyar yana da wani buri ko aƙida. Amsa dai ita ce a'a. Matashin wannan zamani, ya kasance a wani hali ne na matukar damuwa. Dalilin haka shine rashin hangen wata makoma mai haske ga rayuwar sa. Ko da shike baitulmalin ƙasa cike yake da dukiya, amma yan Algeria basa ganin haske a rayuwar su, saboda haka martasan sukan gwammace su zama yan tarzoma ko yan ƙunar-bakin wake.


A ƙasashen Mauretania da Morocco ko a Algeria, ko Tunisia, jama'a suna ƙara nuna fushin su kan shugabanni a sakamakon ƙaruwar talauci da rayuwa cikin halin ƙaƙa-ni-kayi. Burin ƙananan ƙungiyoyi na yan takife, shine su yaki gwamnatoci da shugabannin su da basa komai sai kwashe dukiyar jama'a, su kuma haɗa kansu da ƙungiyoyin tarzoma da suka yi suna a duniya, kamar al-Qaeda. Yar jarida Baya Glacemi tace:


Babu wani dalili da mazauna wannan yanki zasu nuna ƙarfin zuciyar samun haske. Idan har aka ci gaba a wannan halin da ake ciki, ba zan ce Algeria za'a yi asarar ta gaba ɗaya ba, saboda ƙasar tana da kudi mai yawa, to amma ƙasar zata zama gagara-badau, babu mai iya mulkin ta. Idan har aka ci gaba haka, kuma gwamnati ta kasa ɓullo da wani tsari na tattalin arziki ko kyautata zaman jama'a da siyasa, to kuwa bana ganin haske a wannan kasa.


Watakila kuwa a zahiri a hakan za'a ci gaba, domin kuwa a makon jiya ne ma, shugaban Algeria, duk da fama da yake yi da rashin lafiya, yace zai tsaya takara karo na uku, duk da sanin cewar yin hakan zai saɓawa tsarin mulkin ƙasar ta Algeria.