Tarruruka a game da ricin makaman nukleyar Iran | Labarai | DW | 08.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tarruruka a game da ricin makaman nukleyar Iran

Nan gaba a yau ne, ministocin harakokin waje na ƙasashe 5 masu kujerun dindindin, a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, za su sake hawa tebrin shawara, a birnin New York na Amurika, game da rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran.

Kazalika, ƙasahe 15 membobin komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia za suyi nasu taro, domin nazari a kan shawara da France, Amurika, da Britania su ka bayar na waraware wannan rikici.

Jikadan Amurika a Majalisar Dinkin Dunia, John Bolton, ya sanar manema labarai cewa, wannan mahimman taruruka guda 2, za su maida hankali kan matakan bai ɗaya,da ya cencenta a ɗauka, domin magance baddaƙalar rikicin makaman nuklear Iran ,da a halin yanzu, ya zama kanun labarai a fadin dunia.

China da Rasha, na ci gaba da nuna adawa da mattakan da sauran manyan ƙasashe ke bukatar a ɗauka kan Iran.

A dangane da hakan, akwai alamun tarrurukan na yau kamar wanda su ka gabata su watse baran baram.