1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashe 8 da suka fi ƙarfin arziki

May 26, 2011

Shugabannin G8 za su mayar da hanakali a taron birnin Deauville na Faransa kan rikicin ƙasashen larabawa da kuma shugabancin IMF, tare da duba matsalar tashar makamashin nukiliya ta Fukushima da ke Japan.

https://p.dw.com/p/11OIa
Shugabannin manyan ƙasashen duniya lokacin taron 2009 a italiyaHoto: AP

Shugabannin gwamnatoci da kuma ƙasashe takwas da suka fi ƙarfin tattalin arziki a duniya na shirin gudanar da wani taron ƙoli yau alhamis da kuma gobe juma'a a birnin Deauvile na ƙasar Faransa. Daga cikin mahimman batutuwan da za su mayar da hankali akai, har da illar da lalacewar tashar nukuliyar Fukushima da ke Japan ta haifar ma tattalin arziƙin wannan ƙasa.

Kana shugabannin takwas bisa jagorancin Nicolas Sarkozy mai masaukin baƙi, za su sanar da yawan kuɗi da za su tallafa wa ƙasashe larabawa da ke fiskantar guguwar neman sauyi domin sunaiwatar da sauye sauye da za su dace da zamani. Hakazalika sun bayyana aniyar rage wa ƙasashen Tunisia da kuma Masar bashin da suke binsu, da nufin taimaka musu komawa kan tafarkin demokaraɗiya cikin hanzari.

Wani muhimmin batu da ake sa ran zai mamaye taron, shi ne na wanda ya fi dacewa ya maye gurbin shugaban asusun lamini na duniya bayan murabus din Dominique Strauss-kahn. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tuni ta bayyana cewar ɗaukacin ƙasashen Turai za su mara wa ministar kuɗin Faransa wato Christine lagarde baya, bayan da ta sanar cewa za ta yi zawarcin kujerar shugabancin IMF ko FMI.

Ƙasashe takwas da suka fi ƙarfin tattalin arziki a duniya dai, sun haɗa da Amirka, da Canada, da Birtaniya, da Faransa, da Jamus, da Italiya da Japan da kuma Rasha.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu