1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Yankin Gabas ta Tsakiya

September 14, 2010

Shuagabannin Isra'ila da Palasɗiniyawa na ci gaba da tattaunawa

https://p.dw.com/p/PBwx
Hoto: DW-Montage/AP/picture-alliance/dpa

Da alama tattaunawar kai tsaye ta samar da zaman lafiyar da ake yi tsakanin fraministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma shugaban Palasɗiniyawa Mahamoud Abbas a Charm el Cheik a ƙasar Masar ta fara yin tsauri, musamman ma dangane da butun tsaigaita wa'adin ci-gaba da gine ginen da is'raila ke yi a yankunan Yahudawa 'yan kama wuri zauna a gaɓar kogin jordan, wanda aka shirya wa'adin zai cika a ranar 26 ga wannan wata da mu ke ciki.

Tun da farko dai shugabannin Isra'ilan sun ce babu maganar tsawaita wa'adin yayin da kuma palasɗiniyawan suka yi barazanar ficewa daga taron idan har isra'ila ta ci-gaba da ƙaddamar da shirin na gine gine.

Babbar jam'iar diflomasiya ta ƙasar Amurka dake kula da hulɗa da ƙasashen waje da ke jagorantar taron ta yi kira ga sanssan biyu da su yi sulhu.

Mawallafi: Abdurrahaman Hassane

Edita: Abdullahi Tanko Bala