1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron 'yan jarida na Deutsche Welle na 2013

June 17, 2013

Taron kasa da kasa na DW da ya saba gudana a birnin Bonn ya na mayar da hankali a kan rawar da kafafen watsa labarai ke takawa wajen inganta harkokin tattalin arziki a duniya.

https://p.dw.com/p/18rHk
Auf dem Bild: Foyer beim Global Media Forum 2013. 17.6.2013, Bonn. Bild: Martin Koch / DW
Global Media Forum 2013Hoto: DW/M.Koch

Da sanyin safiyar Litinin din nan ce dai aka bude taron na bana wanda ya samu mahalarta da dama daga kasashen daban-daban na duniya musamman kasashen da ke amfani da harsunan nan talatin da tashar DW ke watsa shirye-shiryenta a ciki.Taken taron na bana dai ya mai da hankali ne kan bunkasar tattalin arziki da harkokin watsa labarai wanda za a share kwanaki uku ana gudanar da shi.

Yayin taron dai mahalartansa wanda manema labarai ne daga gidajen talabijin da radiyo da jaridu da kuma masu rubuce-rubuce a shafukan internet, za a tattauna batutuwa da su ka danganci batun tatalin arzki da samawa matsa aikin yi da shugabanci na gari da amfani da kafafen sadarwar internet musamman ma dai na sada zumunta wajen kawo sauyi a tsakankanin al'umma da makamatansu.

Global Media Forum Teilnehmer Erik Bettermann
Shugaban tashar Deutsche WELLE Erik BettermannHoto: DW

Shugaban tashar DW Eric Betterman ya ce bikin na bana ya zo daidai da lokacin da tashar DW ke cika shekaru sittin da kafuwa ta na watsa shirye-shiryenta ga kasashen duniya. Kazalika bikin ya yi daidai da zanga-zangar nan mafi girma da aka yi a tsohuwar Jamus ta adawa da masu mulki gurguzu na wancan lokacin wadda aka yi rana irin ta yau amma a shekarar 1953.

A daura da wannan ne Mr. Betterman ya ke cewar bikin na bana na musamman ne duba da irin aiyyukan da DW ke yi na watsa labarai da 'yancin fadar albarkacin baki wanda al'ummar Jamus a lokacin boren na 1953 suka yi ta rajin ganin an tabbatar da shi.

Da ya juya kan batun shirye-shiryen da DW ke watsawa kuwa wadda ke da ofisoshi a Berlin fadar gwamnatin kasar da kuma birnin Bonn , Mr. Betterman cewa ya yi kafar watsa labaran na maida hankalinta kan batutuwan da su ka danaganci siyasa da kare hakkin dan Adam da kuma kare muradun demokradiyya. Shi kuwa ministan raya al'adu da kafafen watsa labarai na tarayyar Jamus Bernd Neumann a jawabisa yayin bude taron cewa ya yi tashar DW tasha ce ta al'umma.

" DW tasha ce ta al'umma musamman ma dai wadanda ake musgunawa a yankuna daban-daban na duniya domin kuwa ta zame musu wani tsani na kaiwa ga labarun da su ke bukata duba da yadda tashar ke yin aiyyukanta ba tare da katsalandan ba. Tashar dai a baya kai har ma yanzu na maida hankali wajen kare hakkin dan Adam kana wata hanya ce da ke hade kan al'umma daban-daban."

A nasa bangaren magajin garin Bonn Jürgen Nimptsch da ma dai sauran manyan bakin da su ka yi jawabai sun yi tsokaci dangane da irin aiyyuka da tashar DW ta ke yi daga shekaru sittin din da su ka gabata zuwa yau gami da irin rawar da ta taka a wadannan sekaru. A ranar Talata ne za a cigaba taron na Global Media Forum inda mahalartansa za su cigaba da tattaunawa da kuma kan batutuwan da taron ya kunsa, yayin da ake sa ran karkare taron a ranar Laraba idan Allah ya kaimu.

Plenary 1 – Ratings Versus Quality: Media Caught Between Market Pressure and the Mission to Educate © Deutsche Welle/K. Danetzki, 25.06.2012
Mahalarta taron suna zuwa daga sassa daban daban na duniyaHoto: DW/K. Danetzki

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar