Taron yaki da azabtar da mata a spain | Labarai | DW | 27.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron yaki da azabtar da mata a spain

Prime miniter Jose Luis Zapatero na kasar Spain,ya bude wata majalisar gudanar da kamfain din yaki da yiwa mata azabar cikin gida a kasashen turai,inda yace azabtar da mata bashi da matsuguni a kowace alumma ingantacciya.Ya bayyana cewa wulakanci da tozartawa da tsoratarwa ababai ne dake da muni a rayuwar kowane bil adama,musamman mata,wadanda ya kamata a rika tarairayarsu.Premier Zapatero ya fadawa wakilai kimanin 300 dake wakilatar kasashe 46 dake wannan majalisar cewa,azabtar da mata na mai zama nauyin take hakkin biladama daya fi kowane laifi,.Rahotan da majalisar ta fitar na nuni dacewa,kashi guda daya daga cikin 4 na matan turai na fuskantar wani naui na azabtarwa daya shafi jikinsu,akalla sau daya.