Taron yafewa Liberia bashi. | Siyasa | DW | 15.02.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron yafewa Liberia bashi.

Ƙasashen Amurika da Jamus, sun yafe bassusukan da su ka tambayo Liaberia.

default

Kwalliya ta biya kuɗin sabulu, a yunƙurin shugabar Liberia Ellen Sirleaf Johson, na neman ƙasashe masu hannu da shuni, su yafe ɗimbin bassusukan da su ka tambayo ƙasar ta.

A sakamakon taron yini 2, da bankin dunia ta kira, a birnin washington na ƙasar Amurika ne, shugabar ƙasar ta Liberia, ta sami nasara ciwo kan ƙasashe masu hannu da shuni, na su dubi Liberia da idon rahama wajen yafe mata wannan bassusuka da su ka yi mata katutu, su ka kuma hana ta shaƙat ! wajen tada komaɗar tattalin arziki, da yaƙi ya nakasa.

Idan aka ɗauki misalin Amurika, ta alƙawarta shafe bashin da yawan shi, ya kai dalla kussan milion ɗari 4, ga Liberia.

Sannan shugaba Geoges Bush, ya yi kira ga sauran ƙasashe su bi sahun Amurika.

Ba da wata wata ba, Jamus ta amsa wannan kira, inda a nan take! ta ce har lahira, ta yafe bashin dala milion 230, da ta tambayo Liberia, to amma inji shugabar tawagar Jamus da ta halarci taron, yafe bashin bai nu fi, da kawo ƙarshen wahaloli a ƙasar Liberia.

Ta ce :

„Ba daga nan take ba !!! saidai kawai, ƙurraru su ci gaba da aiki, tare da haɗin gwiwar hukumomin Liberia,ta wannan hanya, mu na kyauatta zaton za a kai ga matsayi mai inganci“.

To saidai bassukan ƙasashen 2, ba su taka kara sun karya ba, ta la´akari da jimmilar bashin da ke kannLiberia, wanda yawan shi, ya kai dala kussan milion dubu 4.

Amma kamar yadda shuga Sirleaf Johson ta bayyana, mafi yawan wannan bashi, kuɗi da ruwa ne, wanda su ka taru a tsawan shekaru masu yawa.

Ita ma ministar kuɗi ta ƙasar Liberia, Antoinette Sayeh, ta nuna farin ciki a game da wannan , wanda a cewar ta, wani mataki ne,na cima burin kuɓuto Liberia daga sahun ƙasashe masu fama da talauci:

A yayin da ɗauki magana, wakilin assusun bada lamani na dunia, ya yaba da babbar murya, ƙoƙarin sabin hukumomin Liberia.

 • Kwanan wata 15.02.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwC
 • Kwanan wata 15.02.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwC