1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron WTO kan zagayen taron Doha

Deselaers, Peter (DW Online) July 21, 2008

Wannan taron na zama dama ta ƙarshe wajen cimma wata matsaya kan taron Doha

https://p.dw.com/p/EgCX
Shugaban WTO Pascal LamyHoto: AP

A yau Litinin ministocin ciniki daga ƙasashe kimanin 40 wakilan ƙungiyar ciniki ta duniya WTO suke buɗe zaman taron su a birnin Geneva. Shugaban ƙungiyar ta WTO Pascal Lamy ya bayyana wannan taron da cewa zai zama dama ta ƙarshe a ƙoƙarin cimma matsaya ɗaya game da zagayen taron nan na Doha.


Ko da yake shugaban na WTO Pascal Lamy ya sha faɗan haka amma har wayau ba a cimma yarjejeniya dangane da kawo ƙarshen zagayen taron da ake yiwa laƙabi da taron Doha ba. Yarjejeniyar ta WTO ta tanadi bawa ƙasashe masu tasowa da masu samun bunƙasar tattalin arziki damar sayar da kayakin amfanin gonarsu a ƙasashen masu arziki yayin da su kuma ƙasashe masu tasowan za su buɗe kasuwanninsu ga kayakin masana´antu daga ƙasashe masu arziki. Tun kimanin shekaru bakwai da suka gabata a taronsu na Doha wakilan ƙungiyar kimanin 152 ke yi tattaunawa kan wannan batu. Batun rage yawan tallafin da ƙasashe masu arziki ke bawa manomansu na daga cikin batutun dake hana ruwa gudu. Harald von Witzke masani kan harkar cinikin kayan albarkatun noma na jami´ar birnin Berlin ya ce yanzu lokaci ne da ya dace WTO ta samu mafita.


Ya ce "Ko da yake babu wani sauyi da aka samu amma saboda tashin farashin kayan abinci wataƙila ƙungiyar EU da Amirka da sauran ƙasashe da ke bawa manomansu tallafi, za su goyi da bayan tsarin cinikin kayan amfani gona mai sassauci tsakanin ƙasa da ƙasa."


A duk lokacin da farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi kamar yanzu, manoma na samun isasshen kuɗi. Sai idan farashi ya faɗi ne ƙasashe ke ba da tallafi ta hanyar sayen kayan amfanin gona. Saboda haka yanzu aka rage yawan tallafin.


Tobias Reichert na ƙungiyar German Watch mai zaman kanta, ya bayyana tsarin cinikaiya na yanzu da cewa ƙasashe masu arziki ne kaɗai ke cin gajiyarta.


Ya ce "Har yanzu ana kwaran kasashe masu tasowa a fannin cinikin kayan amfani gona. Ko da yake yanzu an rage yawan tallafi ga kayan amfani gonar da ake sayarwa ketare amma a fakaice ana ci-gaba daba da wannan tallafi wanda ke haddasa rashin adalci a harkar ciniki da gogayya tsakanin kasashe duniya."


A shekara ta 1994 aka kafa kungiyar WTO mai mazauni a birnin Geneva bisa manufar samar da wani tsari na bai daya a fannin ciniki tare da kawad da rashin adalci da shingayen ciniki tsakanin kasa da kasa. To amma har yanzu kwalliya ba ta mayar da kudin sabulu ba.