1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron warware Nuclean Koriya ta arewa

July 17, 2007
https://p.dw.com/p/Btv0
Mohammed Elbaradei
Mohammed ElbaradeiHoto: AP

Gabannin bude taron kasashe shida adangane da warware matsalar shirin Nuclear na koriya ta arewa a birnin Beijing din kasar sin,wakilai sun bayyana fatansu na cimma nasaran cikin kwanaki kalilan masu gabatowa.

Masu tattaunawan wadanda ke cike anashuwa adangane da cimma burinsu na rufe cibiyar nuclear koriya ta rawan wadda ke Yongbyon,sun hallara a birnin Beijing domin kokarin warware matsala babba dake gabansu,na shawo kan Pyangyong ta gabatar dukkan sirrinta na sarrafa makaman atom, wadanda ta dogara kuma take rayuwa akansu.

A yau nedai jakadun kasashen suka fara gudanar da taron share fage na yini biyu.

Wakilin Amurka Chritopher Hill ya fadawa taron manema labaru cewa,ya gabatarwa koriya ta arewan shirin yadda zata gudanar da zagaye na biyu na kwance damarar nata,wanda zata kammala kafin karshen wannan shekara.

A karkashin wannan tsarin inji shi,ana bukatar koriyan ta gabatar da dukkan harkokin nuclearnta, tare da lalata cibiyarta dake Yongbyon.

Mr Hill yace duk dacewa bazai iya magana da yawun koriya ta arewan ba,bisa dukkan alamu zata amince da aiwatar da wadannan bukatu da aka gabatar mata.

Cibiyar ta Yongbyon dai ,nada karfin sarrafa makaman gurneti ,kuma a watan Febrairun daya gabata nedai koriyan ta amince da rufe cibiyar,inda amadadin hakan zaa bata Tonne dubu 50 na mai,wanda kuma aka fara shigar dashi kasar daga koriya ta kudu tun a makon daya gabat.

Rufe cibiyar ta dake Yongbyon dai na mai zama mataki na fatan cewa zaa cimma shawo kan Pyabgyong ta kawo karshen dukkan shirinta na sarrafa makaman nuclear,kamar yadda babban Directa a hukumar kula da yaduwar makaman nuclear ta mdd Mohammed Elbaradei ya bayyana...

“Yace mataki na gaba babu shakka shine bukatar cimma yarjejeniya a wannan taron bangarori shida,adangane da yadda zaa lalata dukkan makaman ,idan har koriya ta arewan ta gabatar da makaman da cibiyoyin sarrafa su.Koda yake hakan zai dauki lokaci mai tsawo.Abu ne mai sarkakkiiyar gaske,domin dole ne mu tabbatar da gaskiyar gabatarwan nata”

Kasashen koriya ta arewa da ta ku da Amurka da japan da Rasha da Sin dai zasu fara mahawara tare da nazarin lalata cibiyar Yongbyon,da kuma dukkan harkokin da suka danganci sarrfa makamai.

Direktan dake kula da lamura da suka shafi nahiyar Asia a kungiyar sasanta rigingimu na kasa da kasa Peter Beck,ya yaba da yadda lamura suke tafiya...

“yace wannan babban cigaba ne ,duk dacewa mun jima muna dakon yiwuwar hakan,duk dacewa wannan nasar ne ,muna da sauran gagarumin aiki agaba.Wannan shine matakin farko,wadanda suka rage sune masu wuya,kuma a yanzu haka bamu swan ko da gaske koriya ta arewan take dangane da kawo karshen makaman nuclearnta ba”