1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron wanzar da zaman lafiya a Iraqi

May 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuMH

A yau a ƙasar Masar ake fara taron yini biyu ta gamaiyar ƙasa da ƙasa wanda ya haɗa da maƙwabtan Iraqi domin gano bakin zaren warware rikicin da yake neman ɗaiɗaita ƙasar da kuma ya jawo hasarar rayukan dubban jamaá, tun bayan da Amurka ta mamaye ƙasar a shekarar 2003. Tuni manyan jakadun ƙasashe da suka haɗa da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice suka isa yankin shakatawa na Sharm el-Sheikh inda zaá gudanar da taron. Za kuma ta haɗu da jakadun ƙasashen larabawa dana China da Rasha da kuma ƙungiyar tarayyar turai. A jiya laraba Condoleezza Rice ta gana da sakataren majalisar ɗinkin duniya Ban Ki-Moon da kuma P/M Iraqi Nuri al-Maliki. Babban batu da ake gani zai ɗau hankali a wajen taron shine tattaunawa tsakanin Condoleezza Rice da Ministan harkokin wajen Iran Manoucher Mouttaki. Ganawar zata zamo matakin ƙololuwa na diplomasiya tsakanin washington da Tehran tun bayan juyin juya halin Islama na ƙasar Iran a shekarar 1979. Amurkan na zargin Iran da haddasa tarzomar dake faruwa a Iraqi, abin da Iran ɗin ta musanta da cewa bashi da tushe balle makama. Muƙaddashin P/M Iraqi Barham Saleh ya baiyana taron da cewa yana da matuƙar muhimmanci wajen samun taimako da goyon bayan maƙwabta da kuma sauran ƙasashen duniya domin ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Iraqi.