1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron wadata ruwa ga Afirka

Ƙasashen Afirka dake fama da ƙarancin ruwa za su yi taro a birnin Njamena na Chadi

default

Yankunan sahel dake fama da ƙarancin ruwa

A cikin wannan makon ne wasu ƙasashen Afirka dake cikin ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel, mai fama da ƙarancin ruwa, zasu gudanar da taro a birnin Njamena na ƙasar Chaɗi, domin nazarin hanyoyin shawo kan matsalolin ƙarancin ruwa da kuma kare al'ummominsu daga matsalar ƙarancin abinci. Wani jami'in gwamnatin ƙasar Chaɗi, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewar, a ranar 25 ga watan Maris ɗinnan ne taron zai gudana, wanda ke da nufin samar da ƙawancen ƙasashen duniya dake yaƙi da kanfon ruwa. A cikin wani daftarin da kwamitin tsara taron ya fitar, ya nunar da cewar, tun a shekara ta 2004 ne aka amince da ƙafa wannan ƙawancen da nufin samar da kuɗaɗen tinƙarar matsalar, tare da baiwa lamarin fifikon daya dace dashi.

Ƙasashen dake cikin ƙungiyar dai, sun haɗa da Burkina Faso, Cape Verde, Chad, Gambia da Guinea-Bissau. Sauran kuwa su ne: Mali, Mauritania, da jamhuriyyar Nijar, da kuma Senegal. Da dama daga cikin ƙasashen dai, na fama da matsalar ƙarancin abinci sakamakon ƙarancin ruwar sama.

A cikin watan maris ɗinnan ne ƙungiyar ƙasashen ta sanar da cewar, Chadi da jamhuriyyar Nijar suna fama da tsananin ƙarancin abinci, abinda kuma yasa miliyoyin jama'a ke fuskantar barazanar nyunwa.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Abdullahi Tanko Bala