1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen yamma na son Assad ya sauka daga mulki

Lateefa Mustapha Ja'afarNovember 13, 2015

Birtaniya ta ce tilas ne shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya sauka daga kan mulki in har ana son shawo kan matsalar rikicin kasar da ke ci gaba da lakume rayuka.

https://p.dw.com/p/1H5VU
Taron kasa da kasa kan rikicin Siriya
Taron kasa da kasa kan rikicin SiriyaHoto: Getty Images/AFP/B. Smialowski

Sakataren harkokin kasashen ketare na Birtaniya Philip Hammond ne ya bayyana hakan a Prague gabanin taron kasa da kasa kan rikicin Siriya da za a gudanar a birnin Vienna, inda ya ce saukar Assad kan karagar mulki na zaman wani bangare na shawo kan rikicin da kuma kafa sabuwar gwamnati a kasar. A nata bangaren da take zantawa da manaema labarai jim kadan bayan da ta gana da Firaministan kasar Ostireliya Malcolm Turnbull shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi.

"Muna bukatar sulhunta rikicin ta hanyar siyasa, a zagaye na biyu na tattaunawar da za mu yi a birnin Vienna za mu gana da masu ruwa da tsaki a rikicin ba wai kawai Rasha da Amirka ba har ma da Saudiya da Iran. Ina fata tattaunawar tamu za ta samar da mafita ta siyasa."

Taron na Vienna da za a gudanar a karshen mako dai zai samu halartar a kallah kasashen duniya 20 da kuma masana na kasa da kasa domin kawo karshen rikicin shekaru biyar din da Siriya ke ciki.