Taron tuntubar juna akan Somalia a Nairobin,Kenya | Labarai | DW | 06.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron tuntubar juna akan Somalia a Nairobin,Kenya

Shugaba Abdullahi Yusuf na kasar Somalia yayi kira dangane da bukatar gaggauta aikewa da dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa ,zuwa wannan kasa da yaki ya daidaita.Shugaban Somalian yayi wannan kira nea a birnin Nairobin kasar Kenya,inda yake halartan kungiyar tuntuba na kasa da kasa a dangane warware rikicin kasarsa,taron dake samun halartan jakadun kasashen turai dana Afrika.Ana kyautata zaton dai dukkan dakrun da zaa aike kasar ta Somalia,zasu kunshi dakaru ne daka kasashen Afrika zalla.A yanzu haka dai kasar Uganda ce kadai,ta bayyana muradinta na bada gudummowan sojojinta.