1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron tuntuɓar juna tsakanin Jamus da Faransa

default

Merkel da Sarkozy da wasu ´yan makaranta a Berlin

Tun bayan boren da baki matasa a Faransa suka tayar a unguwannin dake wajen birnin Paris, an gane cewa Jamus makwabciyar Faransar ta na iya fuskantar irin wannan bore. Don bawa wannan batu muhimmanci ya sa ministocin kasashen biyu suka fice daga zauren taron don yin rangadi a wurare da dama a birnin Berlin . Alal misali ministan aikin noma na Jamus Horst Seehofer da takwaransa na Faransa Michel barnier sun yi rangadi a wata makaranta dake Wedding, wata unguwa a Berlin mai yawan baki a cikinta. Su kuwa ministocin dake kula batutuwa na wasannin motsa jiki wato Schäuble da Alliot-Marie sun ziyarci wata kungiyar wasannin motsa jiki ne dake unguwar ta Wedding. Su ma Merkel da Sarkozy sun yi rangadi a waje.

O-Ton Merkel:

“A yau dukkannenmu biyu mun je wata makaranta inda muka yi tataunawa mai ma´ana da ´yan makaranta Jamusawa da baki a dangane da zaman cude ni in cude ka. Suna cikin shirye shiryen da aka na hadin guiwa tsakanin matasan Jamus da Faransa.”

Ba´a dai bayyana cikakken sakamakon taron na tuntubar juna tsakanin gwamnatocin ba, amma da farko an bawa dukkan ministocin lokaci kafin ganawa ta gaba, da su yi nazari akan wasu shawarwari na samar da wata manufa ta bai daya game da sajewar baki da ´yan kasa. Dukkan sassan biyu sun nuna bukatar rage yawan bakin da ke shiga kasashen dake cikin yarjejeniyar nan ta Schengen, wadanda babu iyakoki tsakanin su.

O-Ton Sarkozy:

Sarkozy ya ce “Zamu samar da wata munafa ta bai daya dangane da zaman baki. Ina amfanin yarjejeniyar Schegen idan muka ci-gaba da aiwatar da manufofin dabam-dabam.”

Tattaunwar ta su ba ta tsaya kan baki da zamantakewa ba, a´a Merkel da Sarkozy sun kuma tabo batun siyasar duniya, musamman kan matakan da za´a dauka kan Iran dangane da shirin ta na nukiliya. Ra´ayi ya zo daya na hade kai da sauran kasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD a kan batun na Iran. Kuma idan kasar ta ki sassautowa to kwamitin sulhu zai zartas da sabon kuduri na sanya mata takunkumi. To amma kafin wannan lokaci Jamus da Faransa zasu kara matsawa Iran lamba inji Merkel.

O-Ton merkel:

“Mun tattauna da juna da ma sauran kasashen Turai cewa sannu a hankali zamu rage huldodin cinikaiyar mu da Iran. Alal misali Jamus ta fara yin haka tare hukumar Hermes wadda ke kula da harkokin kasuwanci da ketare.”

Ko da yake a farko farkon canjin shugabanci a Faransa daga Chirac zuwa Sarkozy an samu sabanin ra´ayi to amma yanzu bisa ga dukkan alamu yanzu an shiga wani kyakyawan yanayi na fahimtar juna tsakanin Berlin da Paris.