Taron Tripolie a game da rikicin Darfur | Labarai | DW | 15.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Tripolie a game da rikicin Darfur

Wakilan ƙasashe da na ƙungiyoyi 18 na ci gaba da zaman taro a birninTripolin ƙasar Libia, a game da rikicin yankin Darrfur.

Burin da mahalarta wannan taro ke buƙatar cimma, ya jiɓanci samar da zaman lahia mai ɗorewa, a wannan yanki da ke fama da tashe tashen hankula, wanda ya zuwa yanzu, su ka hadasa mutuwar mutane fiye da dubu 2, da kuma saka a ƙala mutane milion 2 a cikin halin gudun hijira.

A jawabin sa na buɗe taro, wakilin Majalisar Ɗinkin Dunia Jan Elliason, ya bayana wajibcin samun haɗin kan ƙungiyoyin tawaye daban daban na Darfur, domin gaggauta aika tawagar shigha tsakani, wadda zata ƙunshi sojojin Maljalisar Ɗinkin Dunia da na ƙungiyar Taraya Afrika.

A na sa gefen,wakilin ƙungiyar AU,Salim Ahmed Salim, ya nunar da uƙubar da mazauna yankin Darfur ke ciki, da kuma mahimancin wuce matakin mahaurori.

Gobe idan Allah ya kai mu za a rufe wannan taro, tare da bayyana sanarwar sakamakon da ya cimma.