1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tallafawa kasashe a sweden

Zainab A MohammadSeptember 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5d

kasashe da kungiyoyin bada tallafi ,sun bada gudummowan kimanin euro million 500,wa alummar palasdinawa,wanda ya kunshi dalan Amurka million 55 na hukumar tallafin gaggawa ta mdd.Ministar harkokin tallafin Sweden,kuma mai masaukin bakin dake halartan wannan taroCarin Jamtin,tace wannan kyakkyawan sakamako ne wanda zai tallafawa Palasdine nesa ba kusa ba.Anasaran kimanin dala million 114 daga cikin wannan tallafin ,zai shiga harkoki ne na tallafawa rayuwar alummar yankin,ayayinda zaa amfani da sauran wajen gine gine wuraren more rayuwan alummar ta palasdinawa.Shugaban hukumar kula da agajin gaggawa ta mdd Jan Egeland,ya fadawa maharta taron na Sweden cewa,kungiyar gamayyar turai tayi alkawarin bada gudummowan dala million 64.Mr Egeland yace wannan taron ya haifar da da mai idanu,wanda makasudunsa shine tallafawa alummar Zirin Gaza.Jamiin na mdd ya bayyana muhimmancin wannan taro wajen tallafawa alummar ta opalasdinu,wadanda ke rayuwa cikin kunci.