1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tallafawa Afirka ta Tsakiya

November 17, 2016

Manyan hukumomin duniya da kasashe sun yi alkawarin tallafawa Janhuriyar Afirka ta Tsakiya sake farfadowa daga yakin basasa da ya daidaita kasar.

https://p.dw.com/p/2SpwH
Zentralafrikanische Republik Präsident Touadera
Hoto: picture-alliance/dpa/L. Koula

Shugaba  Faustin-Archange Touadera  ya yi kira ga kasashen duniya da hukumomin agaji da su taimakawa Janhuriyar Afirka ta Tsakiya, daya daga cikin kasashe matalauta da ke kokarin farfadowa daga yakin basasa.

Ya jaddadawa mahalarta taron gidauniyar tallafawa kasar da ke gudana a birinin Brussels cewar, gudunmowar ta su za ta je nesa ba kusa ba wajen farfado da wannan kasa da ke kan tsini, kuma ke hada iyaka da kasashe masu yawa a Afirka.

Tun a shekara ta 2013 ne dai tsohuwar uwargijiyarta Faransa ta taimaka wajen kawo karshen rikicin addini da  Afirka ta Tsakiyar ta fada, kuma a karshen watan da ya gabata ne aka kawo karshen ayyukan sojojin a hukumance. Duk da cewar an yabawa hakan, barkewan sabon rikici ya haifar da fargaba a wasu sassan kasar. A yanzu haka dai akwai dakarun kasa da kasa na Majalisar Dinkin Duniya da MINUSCA na Afirka dubu 10 da ke kula da harkokin tsaro a kasar.

Mahalarta taron gudunmowar sun hada da Kungiyar Tarayyar Turai da MDD da Bankin Duniya da Asusun bada lamuni na duniya watau IMF da Faransa da kuma Amurka.