1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tallafawa Afghanistan a birnin Berlin

Mohammad Nasiru AwalJanuary 31, 2007

Ana gudanar da taron ne don sanin inda aka kwana bayan taron birnin London a bara.

https://p.dw.com/p/BtwR
Shugaba Hamid Karzai
Shugaba Hamid KarzaiHoto: AP

A farkon taron na yini biyu a babban birnin tarayar Jamus Berlin, ministan harkokin wajen Afghanistan Rangeen Dadfar Spanta ya yi korafin cewa ana watsi da gwamnatin Afghanistan a shirye shiryen sake gina kasar bayan shekaru 25 na yake-yake. Ya ce amincewa da hukumomin Afghanistan wani muhimmin mataki ne na fita daga wannan hali da ake ciki. Ya ce ´yan ta´adda ka iya amfani da wannan hali idan gwamnatin Afghanistan ta kasa taimakawa ´yan kasarta.

“Ya kamata mu fahimci cewar za´a iya girke sahihiyar demukiradiya da kwakkwarar gwamnati a Afghanistan, idan muka girmama dokar kasa da kare hakkin dan Adam musamman ma na mata.”

Ana taron ne da nufin kimanta irin ci-gaban da aka samu tun bayan babban taron birnin London a bara, inda gamaiyar kasa da kasa ta kaddamar da wani shiri na shekaru 5 na hade kan taimakon kudi da na soji ga Afghanistan. To sai dai watanni 12 bayan taron na London har yanzu daukacin yankunan kasar na fama da rigingimu yayin da shugaba Hamid Karzai mai samun daurin gindin kasashen yamma ya kasa fadada ikon sa a fadin kasar baki daya.

Ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier wanda kasar sa ke karbar bakoncin taron ya ce hakan ba kwakkwaran dalili ba ne na mayar da hankali kacokan kan karin yawan dakarun kasa da kasa a Afghanistan.

“Dole ne mu hade ayyukan soji da na sake gina kasar don amfanin farar hula.”

Batutuwan guda biyu tamkar dan jimma ne da dan jummai, domin sake gina kasar ba zai yiwu ba sai an tabbatar da tsaro. Musamman a yankunan kudanci da gabashin kasar inda har yanzu ake fama da hare hare na ´yan Taliban. A halin da ake ciki gwamnatin Jamus na shirin tura jiragen saman yaki samfurin Tornados guda 6 zuwa kudancin Afghanistan, amma ta ce ba zata aike da sojojin ta dubu 3 zuwa wannan yanki mai fama da rikici ba.

Ko da yake ministan cinikaiya na Afghanistan Amin Farhang ya gamsu da haka amma ya na sanya dogon buri ga aikin na Jamus.

“Muna fatan cewa gwamnatin Jamus zata ba da gagarumar gudunmawar sake gina kasar mu da kuma ci-gaban ta. Mun fahimci kin da ta yi na tura sojojin kudancin Afghanistan, amma zata saka mana ta hanyar ba da gagarumar gudunmawa sake gina kasar mu.”

Duk da mawuyacin hali da ake ciki, mai masaukin baki, Steinmeier ya roki mahalarta ta taron da ka da su kawad da kai da ci-gaban da ake samu a aikin sake gina Afghanistan kana kuma su ci-gaba da tallafawa kasar.