Taron sunhunta somalia | Labarai | DW | 22.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron sunhunta somalia

A yau ne Sudan da kungiyar gamayyar kasashen Larabawa suka kaddamar da taron sulhunta gwamnatin rikon kwarya da sojojin sakai na islama dake rike da mafi yawan sassan somaliya da birnin mogadisho.Shugaban tawagar kungiyar musulmin da suka je taron dai ya bayyana bukatar mahawara kai tsaye da wakilan gwamnati,ayayinda shugaba Omar Hassan al -Bashir na sudan ,yace zai zai kawo su teburi guda a taron dazaa bude kowane lokaci daga yanzu.Mohammaed Ali Ibrahin ,dake zama wakilin kungiyasr kotunan musulunci na somalin ,ya fadawa manema labaru cewa a shirye suke su fuskanci wakilan gwamnatib ,domin tattauna batun samar da zaman lafiya a somalia.

To sai dai wakilan bangaren gwamnati sunki amincewa da fuskatar yan adawan a wannan taro,inda suka bukaci haduwa dasu acikin somaliyan.Tun da safiyar yau nedai kungiyar kasashen larabawan ta kaddamar da taron komitin sasanta Somalian,wanda ya samu halartan ministocin harkokin wajen kasashen da gwamnatin somalia,amma wakilan kotunan musuluncin basu halarci taron ba.