1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhunta rikicin Somalia

Yahouza S. MadobiFebruary 9, 2007

Komitin da a ka ɗorawa yaunin sulhunta rikicin Somalia, ya yi zaman taro a birnin Dar-es Salam na Tanzania

https://p.dw.com/p/BtwJ
Hoto: AP

Komitin da aka girka domin lalubo mattakan shinfiɗa zaman lahia a ƙasar Somalia, ya yi zaman taron sa, yau a birnin Dares-es Saslam na ƙasar Tanzania.

Wannan komiti ya ƙunshi ƙasashen yankin gabancin Afrika, da wakilan ƙasar Amurika, da na ƙungiyar taraya Turai da na gamayyar Afrika.

Mahimman batutuwan da mahalarta taron su ka tanttana, sun haɗa da hanyoyin samar da zaman lahia mai ɗorewa, a ƙasar Somalia, da ke fama da rikicin tawaye, tare da batun tura dakarun kwantar da tarzoma, na ƙungiyar taraya Afrika.

A lokacin da ta gabatar da jawabin buɗe taron, matamakiyar sakatariyar harakokin wajen Amurika, mai kula da nahiyar Afrika, ta nunar da cewa bayan tura sojojin Afrika, babban yauni ya rataya ga wannan komiti, ya binciko matakan tabbattar da tsaron gwamnati, da al´ummar ƙasa.

Jendayi Frazer, ta kuma yi kira ga ɓangarori daban-daban masu gaba da juna, a Somalia su bada haɗin kai.

Idan dai ba a manta ba,a farkon shekara da mu ke ciki sojojin gwamnatin Ethiopia, tare da haɗin gwiwar gwamnatin riƙwon ƙwarya su ka furgaɗi dakarun kotunan Islama daga Mogadiscio, da sauran biranen da su ka capke.

Saidai har ya zuwa yanzu tsugune ba ta ƙare ba, domin kussan kowace sahia, sai an kai hare-hare a wuware daban daban na wannan ƙasa, inda har ma wasu ke dangata ta, da yar ƙaramar Irak.

Gwamnatin riƙwan ƙwarya na zargin dakarun Islama da kitsa wannan ta´adanci, domin sake tada zaune tsaye a Somalia.

Bugu da ƙari,magoya bayan kotunan Islaman, na ci gaba da shirya zanga-zanga.

A ranar yau laraba, kimanin mutane dubu su ka hito cikin titina, bayan sallar juma´a, inda su ka yi ta rera kalamomin Allahu Akbar, da kuma tofin Allah tsine, ga abunda su ka kira, ƙasashen mamaya.

Sannan sun ƙona tutocin ƙasashen, Amurika Ethipoia Kenya, Uganda Nigeria da Malawi, da su ke zargi da ɗaurewa gwamnatin shugaba Abdoullahi Yusuf gindi.

Masu zanga-zangar, sun sha alwashin sai sun yi fito na fito da dakarun ƙungiyar taraya Afrika, da ake ambata kaiwa a ƙasar somalia.