1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhun ta somalia a khartum

Zainab A MohammadSeptember 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5f

Ayau ne jamian kungiyoyin kotunan Islama dana gwamnatin rikon kwarya na Somalia suka gana da masu shiga tsakani daga kungiyar kasashen larabawa a birnin Khartun din kasar Sudan,akokarin da ake na warware rigingimun wannan kasa.

Masu shiga tsakani daga kungiyar kasashen Larabawan da jamian diplomasiyyan Sudan,wadanda ke daukan nauyin wannan taro zagaye na biyu daya samu jinkiri,sun gudanar da wannan taro ne daban daban da bangarorin biyu dake adawa da juna a jajibirin taron,da a hukumance zaa bude gobe a Khartum.

Majiyar jamian diplomasiyyan na nuni dacewa dukkan bangarorin biyu na mahawara adangane da muhimman ababai da zasu mamaye wannan taro na gobe.Majiyar tace kungiyoyin kotunan Islaman wadanda basu da wakili a gwamnatin rikon kwarya na Somaliyan,sun bayyana muradinsu na samun mukamin prime minista,idan har an cimma yarjejeniya a taron na gobe.Daya daga cikin muhimmin batu da taron zai tattauna dai,shine batun tura dakarun kiyaye zaman lafiya domin tallafawa gwamnatin da bata da madafan iko a kasar,da kuma korafe korafen bangarorin biyu,adangane da bayyana sojojin Habasha dana Eritrea a cikan Somalian.