Taron sulhu tsakanin Koriya ta kudu data arewa
November 14, 2007Talla
Faraministocin Ƙasashen ƙoriya ta arewa data ƙudu sun fara wani taron koli na ƙwanaki uku a birnin Seoul.Taron tsakanin Mr Kim Yong Il da takwaransa na Koriya ta kudu Mr Han Duck-Soo zai mayar da hankaline kann ƙara inganta dangantaka, a tsakanin Ƙasashen biyune.Ragowar batutuwan da shugabannin zasu tattauna sun haɗar da rikicin iyaka a tsakanin Ƙasashen biyu da kuma batu na inganta tattalin arziƙi.Taron a cewar rahotanni, yazo ne wata ɗaya bayan wani taro da shugabannin Ƙasashen biyu suka gudanarne a yankin Pyongyang ne dake Koriya ta arewane.