Taron sulhu tsakanin gwamnatin Uganda da yan tawayen LRA | Labarai | DW | 01.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron sulhu tsakanin gwamnatin Uganda da yan tawayen LRA

A birnin Juba, dake kudancin Sudan, a na ci gaba da tantanawa tsakanin gwamnati Uganda, da yan tawayen LRA na arewancin ƙasar.

Ranar 14 ga watan da mu ke ciki, a ka fara wannan ganawa, amma a ka tashi baran-baram.

A na sa ran, a wannan karo, a gano bakin zaren warware rikicin tawaye, a arewancin ƙasar Uganda, da ya ɗauki tsawan shekaru 20.

Mahalarta taron sulhun na Juba, sun haɗa da sarakunan galgajiya na arewa, yamma da kudanci Uganda, wanda su ma, su ka buƙaci kawo gudummuwa, a yunƙurin da ake, na kawo ƙarshen wannan yaƙi.

A na tantanawar bisa jagorancin mataimakin shugaban yankin kudancin Sudan, Riak Machiar.

A wani mataki kuma na ba zata, shugaban ƙungiyar tawayen LRA, Joseph Konny da kotun ƙasa da ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Dunia ke nema ruwa jallo, ya gana da wakilan gwamnatin ƙasar Uganda.

A farkon watan da mu ke ciki, shugaban ƙasar Uganda Yuweri Museveni, ya alkawarta yin afuwa ga Joseph Konny, muddun a ka samu nasara kawo ƙarshen tawaye a wannan tantanawa.

Ƙungiyar tawayen LRA, na da burin kiffar da shugaban ƙasar Uganda, domin girka tsarin mulki, bisa dogaro da gishiƙƙai 10, na dokokin babban littafin addinin Kristanci wato Bible.

Daga farkon rikicin kawo yanzu, mutane a dubun-dubunnai su ka rasa rayuka, sannan fiye da million 2, su ka shiga gudun hijira.

A jamahuriya Demokradiyar Kongo, a na cikin jiran