Taron sulhu tsakanin Corea ta arewa da ta kudu | Labarai | DW | 16.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron sulhu tsakanin Corea ta arewa da ta kudu

Corea ta kudu da Corea ta arewa, sun hau tebrin shawarwari, da zumar samar da matakan warware rikicin da ya ƙi ci, ya ki cenyewa tsakanin su, tun bayan yakin dunia na 2, da ya yi sanadiyar wargaza ƙasar Corea a gida 2.

Tun bayan shekara ta 2000, da ƙasashen 2, su ka fara tantanawa, wannan shine karo na 4, da su gana da juna.

A satin da ya gabata, magabatan ƙasashen, sun amince da ƙadamar da hanyoyin zirga-zirga, ta jirgin ƙasa, a tsakanin su, daga ranar 25 ga watan da mu ke ciki.

Gananawar da su ka fara yau, zata ɗauki tsawan kwanaki 3, za su anfani da wannan dama, domin tantanawa a kann batutuwan, da su ka raba kawunan ɓangarorin2.