TARON SULHU A BIRNIN BAGADAZA DAKE IRAQI. | Siyasa | DW | 30.08.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TARON SULHU A BIRNIN BAGADAZA DAKE IRAQI.

Kakakin ministan cikin gidan iraqi,Col Adnan Abdurrahman,ya bayyana cewa babu wani daya samu rauni ko kuma ya rasa ransa a wani hari da yan tawaye suka kai a safiyar yau litinin a birnin bagadaza.

Wasu yan bindiga dadi kuma a daren jiya suka tasarwa motar wani babban jamiin gwamnatin kasar mai kula da harkokin shiawa,Sheik Hassan Baraka,da harbe harbe,a yayin daya ke hanyarsa ta zuwa wani taron addini a garin karbala,masu tsaron lafiyarsa biyu ne suka rasa rayuikan su sakamakon hakan.

A jiya ne aka fara gudanar da wata tattaunawa tsakanin jamian sojin amurka da kuma magoya bayan Muqtadr Sadr,don samo hanyoyin kawo karshen rikice rikicen dake faruwa tsakanin su.

Bisa dukkan alamu dai baa fara taron da saa ba domin kuwa bukatar farko da magoya bayan Sadr suka nuna itace sojin amurka su fita daga iraqi,wanda kuma wadannan jamiai suka ki amincewa da hakan.

Can kuma a basra jamian sojin britaniya suma sun fara tattaunawa da magoya bayan Muqtadr Sadr dake basran,inda suma ake ta samun rashin jituwa tsakanin su.

An dai samu kawo karshen rikicin najaf daya dauki tsawon makwanni uku ana gwabzawa,sai dai har yanzu ana fuskantar tashe tashen hankula a wasu garuruwan daban daban,wanda kuma bisa hakan ne aka fara tattaunawa tsakanin shiawan da yan siyasa da jamian gwamnati da jamian amurka da kuma sauran manyan shugabannin kasar ta iraqi.

Naim Albakhati,daya daga cikin shugabannin dake jagorantar taron ya bayyanawa mahalarta taron cewa zaa yi gyara a garin najaf da rikici ya illata,sannan kuma sojin amurka zasu fita daga garin sai dai zasu iya kai shawagi don gudanar da ayyukansu.

Ya kuma cigaba da cewa zaa tura yan sandan iraqi najaf,don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.sai dai bai ce komai ba game da batun mika makaman shiawa ga gwamnatin kasar iraqin.

Wani jamiin kiwon lafiya a garin sadr Saad Alamili ya tabbatar da cewa jiya lahadi an samu tsagaitawar rikici a garin sai dai an rasa rayuka goma tare da wasu dari da ashirin da suka samu raunuka a ranar asabar.

Shi kuwa Major Charlie Mayor wani babban jamiin britaniya dake iraqi,wanda kuma ke cikin mahalarta taron dake gudana a bagadaza,ya bayyabnawa manema labarai makasudin wannan taro,inda yake cewa zaa yi wannan taro ne don daukar matakan kawo karshen dukkan rikice rikicen kasar baki daya ba wai kawai rikicin najaf ba.

Haka kuma zaa saurari bukatun shiawan dake yakar sojin amurka don samar da wata yarjejeniya tsakanin su.sannan kuma a duba yiwuwar biyan diyyar wadanda aka ritsa dasu a rikice rikicen kwanan nan.

A yayin da ake wannan tattaunawa,shi kuwa shugaba Goerge W.Bush na amurka ya nuna nadamar sa kann halin da kasar ta iraqi ke ciki,yace amurka tayi zargin Saddam Hussein da kera makamai masu sanya guba.

Shugaba Bush da a yanzu yake neman tazarce a kujerar mulkin kasar tasa yace sun yi wannan zargi ne don ganin Saddam mutum ne da zai iya kera wadannan makamai.sai dai amurka takai harin ne ba tare da duba abin da hakan zai haifar ba.

A wani labarin kuma shugaban kasar faransa Jacque Chirac,ya tura ministan harkokin wajensa Micheal Banier izuwa kasar iraqi,don tattaunawa da yan tawayen da suka yi garkuwa da yan jaridu biyu yan kasar faransa tare da neman faransan ta janye dokar da ta kafa na hana sanya dankwali a makarantun kasar.

 • Kwanan wata 30.08.2004
 • Mawallafi Maryam L.Dalhatu.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvgw
 • Kwanan wata 30.08.2004
 • Mawallafi Maryam L.Dalhatu.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvgw