1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhu a Arusha

August 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuEW

Kungiyoyin yan tawayen lardin Darfur guda 8 ne suka cimma matsaya guda,adangane da cimma sulhu da gwamnatin Khartum,akarshen tattaunawar yini uku,daya gudana a birnin Arushan kasar Tanzania.Manazarta na ganin cewa ,wannan dai wata madafa ce aka cimmawa a dangane da kokarin da akeyi na gano bakin zaren warware rikicin dayaki ci yaki cinyewa na tsawon shekaru 4 da rabi, a lardin na Darfur.A makon daya gabata nedai komitin sulhun mdd ya amince da tura dakarun hadin gwiwa kimanin dubu 26,zuwa lwannan Lardi.Wakilan kungiyoyin yan tawayen a tattaunawar da birnin Rusha dai, sun gabatar da matsaya guda dangane da rabon madafan iko, da albarkatu da tsarin tsaro ,da kuma batutuwa da suka shafi kariya da kyautata rayuwar alummominsu.

Yan tawayen sun kuma bada shawarar a gudanar da taro na karshe nanda watanni biyu zuwa uku masu gabatowa,adangane da wannan batu da suka gabatar.